Talata 29 Satumba 2026 - 21:34
Ilimin Iyali | Daga Ina Tarbiyyar Dabi'u da Sha'awa ke Farawa?

Akwai wata tazara da ke ci gaba da wanzuwa tsakanin al'ummarmu da mahangar Alƙur'ani a fannin tarbiyya, wadda take bukatar gyara. A maimakon shagaltar da iyaye da dabarun gefe ko na'urori kawai, dole ne a mayar da hankali kan babbar hanyar da Alƙur'ani da Sunnah suka shimfida.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza  | Tarbiyar yaro ba kawai bayar da bayanai da dabarun baki ba ne; tarbiyya mika imani da kyawawan halaye ne daga zuciya zuwa zuciya. Iyayen da ba su tsarkake kawukansu ba, ba sa ambaton Allah, kuma ba su da taƙawa a rayuwarsu, ta yaya za su iya raya fiɗirar imani da ke cikin zukatan 'ya'yansu? Alƙur'ani mai girma yana cewa:  

«وَمَنْ یُؤْمِنْ بِاللَّهِ یَهْدِ قَلْبَهُ»

"Kuma duk wanda ya yi imani da Allah, (Allah) zai shiryar da zuciyarsa." (Suratut Taghabun: 11).

Idan kana son zuciyar ɗanka ta shiryu, to da farko miƙa taka zuciyar ga Allah.

 Shimfiɗa: Ƙalubalen Zamanin Intanet

A yau, iyalai suna rayuwa ne a wani yanayi da dukkan shingaye na al'adu suka rushe; yara da matasa suna fuskantar kwararar gurbatattun abubuwa da abubuwan tada sha'awa a kafafen sada zumunta ba tare da shamaki ba. A irin wannan yanayi, "tarbiyyar sha'awa da tsare dabi'u" ba wani abu ba ne na zabi, a'a, wajibi ne na rayuwa domin kare lafiyar zuriya mai zuwa. Sakaci a wannan fage yana da mummunan sakamako, musamman yadda masu son gurbata tarbiyya suke zuba dukkan karfinsu wajen karkatar da matasa. 

Dangane da wannan maudu'i mai muhimmanci, Hujjatul Islam Wal Muslimin Muhsin Abbasi-Waladi ya gabatar da wasu muhimman darussa da mahanga mai zurfi, wadanda suka dace da kowane mai kishin tarbiyya.

Ba Za A Iya Tarbiyya Ba Sai da Alƙur'ani

Duk wanda yake son yin tarbiyya ta gaskiya, to ya sani ba zai yiwu a yi ta ba tare da Alƙur'ani ba, domin Alƙur'ani shi ne ginshiƙin tarbiyya. Allah Madaukakin Sarki yana cewa a cikin Suratul Hujurat, aya ta 7:  

«...وَ لکِنَّ اللّهَ حَبَّبَ إِلَیْکُمُ الْإِیما و نَزَیَّنَهُ فِی قُلُوبِکُمْ وَ کَرَّهَ إِلَیْکُمُ الْکُفْرَ وَ الْفُسُوقَ وَ الْعِصْیانَ...»

"Sai dai kuma Allah Ya sanya imani ya zama abin so a gare ku, kuma Ya kawata shi a cikin zukatanku, kuma Ya sanya kafirci da fasiƙanci da saɓo suka zama abin ƙyama a gare ku..."

An halicci ɗan adam ne a kan wani babban jari na asali, wato "fiɗira" (dabi'ar asali ta son gaskiya). Yaro ba ya zuwa duniya hannu wofi; yana zuwa ne da son Allah da kuma ƙyamar saɓo a cikin zuciyarsa. Sai dai idan aka toshe wannan tafarki na fiɗira ko aka gurbata shi, a lokacin ne mutum zai kyamaci imani kuma ya karkata ga barna. 

Idan muna son kare 'ya'yanmu daga gurbacewar sha'awa, dole ne mu karfafa wannan imani na cikin zuciya. Kuma wannan aiki ba ya farawa da dabaru ko fasahohi; yana farawa ne daga gyara kan iyaye da farko.

Kana Son Karfafa Imanin Danka? Fara da Naka Imanin!

Amirul Muminina Ali (A.S) yana cewa a Hikima ta 73 a cikin Nahjul Balagha: "Duk wanda ya sanya kansa a matsayin shugaba ko jagora ga mutane, to ya fara ladabtar da kansa kafin ya ladabtar da wasu; kuma ya koyar da mutane da dabi'arsa da halinsa kafin ya koyar da su da harshensa."

Tarbiyantar da wasu kaya ne mai matukar nauyi wanda Annabawa suka dauka. Kuskure ne a dauki dan adam a matsayin wata na'ura da za a iya sarrafa shi kawai ta hanyar latsa madanni ko tsara wasu dokoki na waje. Mutum yana bukatar ruhi mai karfi domin ya zama mai tarbiyya, kuma ruhi ba ya samun karfi sai ta hanyar alaka da Allah da nisantar zunubai.

Iyaye ba za su iya cewa yaronsu ya kame idonsa daga kallon haramun a intanet ba, alhali su kansu ba sa iya kame harsunansu daga gulma, karya, ko cutar da mutane. Idan iyaye suna aikata zunubi, imaninsu yana raunana, kuma ruhinsu yana rasa kwarjini da hasken Ubangiji.

 Me Ya Sa Gyaran Kai (Tahzibul Nafs) Ya Zama Wajibi Wajen Tarbiyya?

Akwai dalilai guda hudu da suka sa ya zama wajibi iyaye su gyara kansu kafin su tarbiyantar:

1. Raya fiɗirar Yaro Ta Hanyar Aiki:  

Kyakkyawan halin iyaye yana jawo yara zuwa ga kyawawan dabi'u a dabi'ance. Imam Sadik (A.S) ya ce: "Ku zama masu kira zuwa gare mu ta hanyar nisantar abubuwan da Allah Ya haramta da bin yardarSa; domin idan kuka kasance haka, mutane za su karkata zuwa gare mu da sauri." Idan gida ya cika da kamshin takawa, fiɗirar yara za ta bunkasa cikin sauki.

2. Tasirin Magana a Zuciya:

Maganar da ta fito daga zuciya mai tsoron Allah tana shiga zuciyar mai saurare. Amma kamar yadda Imam Sadik (A.S) ya bayyana: "Idan malami bai yi aiki da iliminsa ba, wa'azinsa yana zamewa ne daga zukatan mutane kamar yadda ruwan sama yake zamewa a kan dutse mai santsi."

3. Ƙarfin Ruhi Don Daukar Nauyin Tarbiyya:

Tarbiyya tana bukatar juriya da karfin ruhi, wanda ba ya samuwa sai ta hanyar kusanci da Allah da nisantar gurbacewar zuciya.

4. Neman Taimakon Ubangiji a Lokutan Rudani:  

Dan adam ba kamar mota ba ne da kanikanci zai iya gano matsalarsa a kan matakai daya-biyu-uku. Halayyar dan adam tana da sarkakiya da banbanci; abin da ya yi aiki a kan yaro na fari ba lallai ya yi aiki a kan na biyu ba. A lokacin da iyaye suka shiga rudani kan wane mataki ya dace su dauka, suna bukatar ilhama da taimakon Allah. Alƙur'ani yana cewa:  

 «یا أَیُّهَا الَّذِینَ آمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ یَجْعَلْ لَکُمْ فُرْقاناً...»

"Ya ku wadanda suka yi imani! Idan kuka bi Allah da takawa, zai sanya muku mararraba (Furqan – basirar rarrabe daidai da kuskure)..."(Suratul Anfal: 29).

 Aiki da Ilimi: Mabudin Karuwar Ilimi da Mafita

Duk wanda ya yi aiki da abin da ya sani, Allah zai yaye masa abin da bai sani ba. Hadisi ya tabbatar da cewa duk wanda ya yi aiki da abin da ya sani, Allah zai koya masa ilimin abin da bai sani ba.

Haka kuma Imam Sadik (A.S) yana cewa: "Ilimi yana tare da aiki; duk wanda ya sani zai yi aiki, kuma duk wanda ya yi aiki zai kara sani. Ilimi yana kiran aiki ne: idan aikin ya amsa masa (sai ya tabbata), idan kuwa bai amsa ba, sai ya yi hijira ya tafi."

Idan mutum ya ki aiki da iliminsa na gyaran kai, to zai ci gaba da zama a cikin rudanin "me zan yi yanzu?", koda kuwa ya karanta dubban littattafan tarbiyya na yammacin duniya.

Komawa Zuwa Ga Asali da Neman Agaji (Tawassuli)

Akwai wata tazara da ke ci gaba da wanzuwa tsakanin al'ummarmu da mahangar Alƙur'ani a fannin tarbiyya, wadda take bukatar gyara. A maimakon shagaltar da iyaye da dabarun gefe ko na'urori kawai, dole ne a mayar da hankali kan babbar hanyar da Alƙur'ani da Sunnah suka shimfida.

A karshe, sauke nauyin tarbiyya a wannan zamani abu ne mai girma da ke bukatar addu'a da neman agajin Ubangiji. Don haka, wajibi ne a kowane mataki—musamman wajen tsare zuriya—a sanya neman ceto da tawassuli da Imamuz Zaman (Allah Ya gaggauta bayyanarsa), wanda shi ne Shugabanmu mai rai kuma kofa zuwa ga rahamar Allah, a sahun gaba na rayuwarmu.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha